MALIKA MALIK CHAPTER 15 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 15 BY JANAFTY
MALIKA MALIK CHAPTER 15  BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng  Shigowar Su Malika ne ya dakatar da Saleem daga,d’aga hannun dayayi zai Naushi Bakin Zahra,wacce ta Sulale kasa tana kuka hannunta Rufe da bakinta tana makyarkyarta. Malika ko Wajen Ayda ta nufa cikin Rawan jiki ta dauketa tana jijjigata batama kai ga Zarafin mgana ba,Taji muryan Saleem cikin wani yanayi yana Fadin”Why..? Zahra me nayi miki..? Me malika ta tsare miki..? Wani alhaKi Yar jaririya Ayda tayi miki da kikeson kasheta.?.”Atare joda da Malika suka kwalolo ido suna bin Zahra da kallo Wacce ke girgiza kai tana kuka take Fadin   “Wlh batamin komai,Sharrin Shedan ne,ammh ni ko kuda Bazan iya kashewa ba..”Tafada tana gunjin kuka tana daga hannuwanta,Saleem bai iya mata mgana ba,sai da Numfashinsa ya koma daidai kafin yace”Hakane bakomai,Allah nagani ban Aureki da Wata Zuciya ba zahra,nayi kokarin ki zama mace tagari hakan ya gagara Daga karshema Saboda bakin kishinki kamaki nayi kina neman kashe yar Jaririyar Allah Wacce…