MALIKA MALIK CHAPTER 13 BY JANAFTY MALIKA MALIK CHAPTER 13 BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng Kwabe Fuska tayi tana wani kif-kifta ido tace”Kamar ya marabana da tsirara kadan ne? Yo inace bakai ka kirani ba,kuma laifi ne don mace tazo Turakar mijinta tana kama da Tsirara kamar yadda kace..”,Tafada tana jifan Malika da wani matsiyan kallo na zakiji ubanki ne,ke kikafi bani haushi. Wani miyau Saleem ya hadiye yana Fadin”a’a ni bance ba,kariso dama na kiraki ne, don kizo na gabatar dake ga malika na kuma taraku nayi muki nasihan zama lafiya da juna kamar yadda al’ada ya tanadar..”Tabe baki tayi kafin ta kariso tana wani jijjigen jiki kamar wata mara hankali,gefen gado ta zauna tana kada kafa,Fuskar na gefe tace”Ina jinka yi da jiki don inajin barci gaskiya..” Daga Saleem din Har Malikan da kallon tababbiya suka bita,tun ballatana ma Malika wacce take ganin alamomin zahra kamar wata bakauyiya wacce batayi ilimi ba,Saleem ne yaga iskancin nata yayi yawa shiyasa ya hade rai kafin ya fara gabatar musu da juna,ya gangaro z…