MALIKA MALIK CHAPTER 12 BY JANAFTY MALIKA MALIK CHAPTER 12 BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng Abangaren gidansu Zahra ne Shirye Shiryen yafi yawa saboda itace uwar gayyah,Tun ana saura sati daya biki Hajiya Saratu momi ta dauko hayar wata Falmata mai gyara amare daga maiduguri,wacce zata gyara Zahra ciki da bai kafin ranar bikin yazo,Hakika bakaramin burgeta momi tayi ba,haka takasa boye murnata afili dama ita burinta taje ta rikita Saleem wanda zai manta da kowa da komai sai ita shalele Fatimatul zahra’u. Bangaren gidansu Saleem kuwa Abbi shima ya saki aljihu ana ta Shiryen shiryen biki,Tunda daga kano Abuja za’a kawo zahra sai ta kwana washegari su Wuto zamfara da ita,wannan Auren na musamman ne,domin yazoma Saleema akan gaba,sun gama Final Exams dinsu ta tararro ta dawo gida aka Shiga shagali da ita tayi alqawari sai ta chusama Malika haushi Sosai da sosai,Balle ma Da Sadiq ya sanar da ita itama Zahran ba baya ba akwai kyau ga iya kwalliya da Iya tsara kalamai,Kawai sai taji lokaci ta burgeta saboda neman suna ha…