ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Dariya ta yi nan suka rankaya zuwa gidan kakaninsu inda Fadeelah take sauka idan sun zo. Fiye da mintuna talatin suna tare daga nan suka yi sallama ganin dare ya fara. Har za ta wuce gida sai wata zuciyar ta ce ta dan leka ta ga jikin Rauda mana tunda dama ta ce Za ta dawo. Lokacin da ta shiga falon su Na’im kawai ta gani a falo suna kallo ta tambaye su ya jikin Ya Rauda suka ce tana ciki ta tashi, Ya Abba yana dakinta yana mata fada ta ki cin abinci. Da sauri ta karasa don su hadu su yi mata fada, tana zuwa bakin kofa ta ji muryar Ya Abba yana Cewa. Rauda hakurin nan da dangana shi ne mafita gare ki, ki cire dukkan damuwarki ki karbi kaddara cewa Samcer baya cikin kaddararki kamar yadda nima na hakura da ita, ki saka haka a ranki cewa Sameer ya yi miki nisa. Ki daure ki cire son shi a ranki duk da kuwa na san kina bakin kokarin ki. Cikin kuka ta cc, Ya Abba na kasa hakuri da son da nake yi wa Yaya Sameer dole na ha…