ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Babbar damuwarsa shi ne yadda ya kasa gano kan Miss Haana dinsa, sam ta ki ta ba shi time ko bare har su yi magana. Zuciyarsa tafi saka masa ccwa Ya Abba ne ya Zuga ta karfi da yaji ya nunawa duniya cewa ya bar masa amma yabi ta karkashin kasa yana yaki da shi cikin ruwan sanyi yadda babu wanda zai gane me yake faruwa. Nasa tunanin kenan don haka ya yankewa ransa yau zai nemi Ya Abba ya fada masa magana mai zafi don ya ji irin abin da yake ji shi ma cikin ransa. Fadeelah kuwa murnarta na son komawa cıkı, domin tun zuwan su Ya Muhammad tunda suka hadu ranar da suka zo har kawo yau da suka kwana biyu ba ta sake ganin fuskarsa ba duk ta tashi hankalina Ya Abdul ne kadai ke kwantar mata da hankali. Cikin damuwa ta ce, “Ya Abdul don Allah wai me yake faruwa Ya Muhammad yake boye min ka san har yanzu ya ki bari mu hadu ko wani laifi na yi masa ne? Fadeelah ban san dalili ba me ye naki na daga hankalinki bayan kun san ba z…