ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya Dariya ya saka ya ce, “Hohoho! Haaya ban san lokacin da za ki daina abu kamar su Amal ba to tashi ki mu je ki dauko min abin da na aike ki ki zo mu zanta da ke ina son jin abubuwa alot a cikin family din mu tun zuwanku har kawo yau don yanzu ke ce ‘yar gida yanzu na san kina da labarin komai da kowa na family dinmu. Murmushi ta yi kamar ba ta da wata damuwa ta ce, “Za ka ji komai kuwa Yayana. Shi ma dariyar ya yi ya kama hannaycmenta ya langwabe har da wani cewa. “Wash! Shi kuma ya ce, ‘Sannu yi a hankali. Kai tsaye dakin Granny ta nufa da ta shigo gidan, ko sallama ba ta yi ba ta kutso kai. Zaune ta iske Granny kan sallaya ta idar da Shafa’l da Wuturi tana shafa addu’a tana shigowa ciki. Kai tsaye ta fara magana cikin daga murya, Granny wane irin laifi na yi muku da za ku yi min haka ke, Ammi, Abba, Mamah Me, Ya Abba da Rauda ku dukkan nan da na lissafa ko ne komai na farin cikina, kukana, dariyata, rayuwata, Www.b…