ZUMA CHAPTER 12 BY SHATUUU ZUMA CHAPTER 12 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng Security din mu da kanshi ya leko ya sanar dani zuwan Yusuf, se lokacin na tuna na bar wayata a daki tana chaji ni kuma na fito parlor Muna assignment dasu, lubna nace tazo muje Zan karba sako, Nawwara na fadin ” Nidai kwana biyunnan you acting strange” Hararta nayi muka saka hijab muka fita, yana tsaye jikin motar Daddy Dan dama nace masa ya shigo dashi ciki, gurin akwai yalwatuwar haske hakan ya bamu damar yiwa juna kallon kallo, sure Ina ganin shi na fahimci daga inda yake, a lokacin tabbas naga kamar su da Abban su amma da Zama yayi Zama se naga kawai jini ne, jikina yayi sanyi saboda zuwan shi ya fara tabbatar min da zargin da nake akan baban shi, kada fa so na yake? To idan so na yake ta Yaya Zan Kai kaina gidan shi na zauna da matar data haife ni matsayin kishiya? ….. ” Babbar Anty barka da fitowa, Ina wuni?” Ya fada yana durkusawa har kasa, innanlillahi na furta gaba daya kunya kamar zata saka na nutse, lubna Kam da a baya na…