ZUMA CHAPTER 10 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 10 BY SHATUUU
ZUMA CHAPTER 10 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Kamar yadda Daddy yayiwa Hibba alkawari personally akan ranar monday zai barni na tafi bikin, hakan ya kasance. Wajen karfe daya muka dauki hanyar kano ni da driver dake kaimu unguwau, tunda na shiga motar nake bacci saboda kwana biyu bana samun isasshen bacci inayi, gaba daya na rame na lalace, idan ka kalleni ko baka tambaya ba zakaga yadda damuwa take kwance saman fuskata, it’s boldly written all over. Seda muka shigo kano sannan na farka sabida hold up da akeyi tun daga round about na mega station, kallon ko ina nake ina tuna dukkan memories din garin baki daya, gashi dai ko wata banyi da barin garin ba, amma abubuwan da suka faru a wannan kwanakin bana tunanin akwai abinda zai goge su daga cikin zuciyata, fact that Sahibi ko kuma Aliyu tunda bai cancanci na kira shi da wani sunan soyayya ba yace na yaudare shi, bayan sacrifices din da nayi making da kuma compromising abubuwa da dama da nayi kawai dan naga relationship din mu …