ZAFIN RABO CHAPTER 4 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 4 BY SAKIEYY
ZAFIN RABO CHAPTER 4 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng  Sakeena bata koma gida ba sai kusan 9 na dare, yanzu hankalinta ya kwanta tun bayan maganar da hamida tayi mata, ita kuwa ba abunda zata ce ma da k’awartata sai dai Allah ya biya ta, da bata da hamida a duniya bata san yarda zatayi ba. Tana shiga d’akin ta taji wayar ta na ringing wacce ta bari a kan gado tayi gidan hamida, saurin k’arasawa wurin ta tayi kanta katse, tana isa ta d’auka sai ga sunan shaheeda a kan screen d’in, ji tayi gabanta yayi mumunar fad’uwa, a hankali ta latsa kan green button d’in tare da saka wayar a kunnanta, sallama tayi bayan ta samu wuri akan gadon ta ta zauna, + “Da aka cemun kina nema na a waya har da cewa in nemi ki in wayata ta dawo abun ba k’aramin mamaki ya bani ba” Abunda shaheeda ta fara ce mata kenan ko sallamar da tayi bata amsa ba, Sakeena wata harara ta saki sai kace shaheedar na gabanta, “Ke bakya amsa sallama ne?” Shaheeda dariya ta saki, “daman shirin da muke har ya kai mu amsa sallamar j…