ZAFIN RABO CHAPTER 2 BY SAKIEYY

ZAFIN RABO CHAPTER 2 BY SAKIEYY
ZAFIN RABO CHAPTER 2 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng  Jogging ya fito yi a harabar gidan, kunnan shi d’auke da AirPods yana jin karatun qur’ani, ya d’an jima yanayi saboda gidan akwai girma sosai, sai da ya gama tsab sannan ya wuce side d’inshi, yana shiga parlor d’inshi ya fara cire shirt d’inshi ya zarce bedroom d’inshi, direct bathroom d’inshi yayi, sai da ya gama wankan shi tsab sannan ya fito d’aure da towel a jikin shi, wurin dressing mirror d’inshi yayi ya fara yin abunda ya zaman mishi al’adarsa, sannan ya wuce closet d’inshi, shiga yayi cikin sweatpants bak’i da bak’ar shirt dan yau kawai zaman gida zaiyi ba wani wuri zaije ba, wurin mekeken standing mirror d’inshi yayi sannan ya fara taje kanshi, sai da ya gama shiryawa tsab tara da feshe jikin shi da turaruka masu dad’in k’amshi sannan ya d’auki wayar shi ya fito daga bedroom d’in, ko da ya iso parlor d’inshi, bai d’aga ido ya kalli k’aton hotan nan ba balle har ya kai idonshi wurin bedroom d’in da yake kallan nashi, …