ZAFIN RABO CHAPTER 1 BY SAKIEYY ZAFIN RABO CHAPTER 1 BY SAKIEYY Www.bankinhausanovels.com.ng Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai. + Kaiwa da kawowa ake a cikin makeken gidan minister d’innan da yake a unguwar maitama a garin Abuja, gidan cike yake da y’an uwa da abokan arziki, fuskar kowa ka gani a cikin gidan tana d’auke da farin ciki da anushuwa, dan yau ne za’ayi babban bak’o, A makeken parlor din gidan duka bakin suka zazzauna da yake dukkan su mata ne, ga kowa yayi kyau yayi shigarsa ta alfarma, barin ma matar gidan Hajia Rahima, wacce yau zuciyar ta k’al take d’auke da tsan tsan nishad’i kamar amma ta alkwari da gidan Aljanna. 1 “Yau ne dawowar babban d’an mu, wanda shekara da shekaru bai tako k’asar Nigeria ba, ni kaina da nake uwar d’akinsa bansa shi a cikin idanuna ba har na tsawan shekaru takwas, dan haka dole ne yau mu ci, mu sha kuma mu rawsaya, mu ragaje, muyi shoki dan kawai mu nuna farin cikin mu, ko ya kuka ce y’an uwa?” Hajia laraba wacce take babbar aminyar matar gidan tayi jawabin tare da k’arashe mag…