UMM ADIYYAH CHAPTER 78 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 78 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng “Eh! Sorry yanzu za mu dawo. Ki kwanta da hankalinki, Twinkle.” Ajiyar zuciya ta yi ta koma ta zauna a cikin ku- jerar, amma ba wani zancen kwanciyar hankali’ har yanzu cikinta juyi yake yi. Daman ya iya wasa da mota haka? Gefenta ta dan kalla a fakaice, ta ga a natse yake tafiya ko a jikin sa, kamar ma ba shi bane ya kusa wurgar da su a titi yanzu. “Noorie, wane wata aka haife ni?” Juyowa ya yi ya dubeta, goshinsa a tattare cikin alamar rudani, “October, Me ya faru?” “Ba komai, kawai ina dubawa ne ko ka na cikin hayyacinka.” Dariya ya yi ya girgiza kai. “Za ki san wannan cikin kankanin lokaci.” Ba ta amsa masa ba, suka ci-gaba da tafiya, tana kallon hanya hade da sake-saken abubuwan da ya kamata ta yi tana komawa gida, saboda shirin liyafar da za su yi nan da kwanaki hudu. Kallon gefen hanya take yi lokacin da suka fara rage tafiya, suna shiga tsukun unguwar, ta muskuta a kujerarta, suna tsayawa a gaban gate, ta hango Rabilu. Sai a lokaci…