UMM ADIYYAH CHAPTER 76 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 76 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng bayan an san ya shigo gidan?” “Sai meye to? Don su wa aka taru? Abeg, tashi mu je. Wallahi ko na kira Maami a waya na ce tun yau kin fara gardama.” “Ke kaska ce wasu lokutan, Allah.” “Oho, dai aje a kula min da Yaya.” Maryamm dai ba ta matsa ba, sai da Umm Adiyya ta mike ta taka mata baya, suka fito zuwa sashen Modibbo, wanda dole sai an ratsa ta tsakar gidan a cimma bangaren, ai tsiya kam ta sha kala-kala wai za ta kuwa ganin ango. Kanta na kasa har suka isa kofar falon. Ya sha gyara, kai ba za ka ce falon tsoho bane wanda ya kai casa’in. Darduma ce a shim- fide mai laushi, ga fulullunkan tumtum an kawata wurin da su, sai kuma ku- jrerun da suka zagaye falon, a bangare guda kuwa takardunsa ne a jere reras a cikin kwaba. Tana shiga idanunta suka fada kansa, take ta ji duniyar ta tsaya cak! Ta mance da masu mata tsiya, ba ta jin komai ba ta ganin kowa sai Zaid Abdur-Rahman, wanda yake tsaye cikin babbar riga da ‘yar cikinta, …