UMM ADIYYAH CHAPTER 75 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 75 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Suna kammala wayar ne, ta fito falon Hajja Ku, nan ta tarar ana shigewa daya dakin da bokitai biyu masu tururi, sai kamshin da ke tasowa daga hayakin. “Hajja ce ta ce a shigo miki da shi, idan kin shirya.” Mai aikin Hajja Ku ta fada. “Idan na shirya me?” Muryar Hajja Kubitto ta juyo tana cewa, “Yau za a fara saka ki a lalle, ba kya dai tsammanin mu kaiwa miji ke haka, ba gyara ba kimtsi ko? Mu ba a mana haka ba, don haka ba za mu sa idanu ayi miki haka ba. Ga nan wadannan bokitan dafaffen Lalle ne da ganyen magarya, masu kyau Www.bankinhausanovels.com.ng da tsafta, ki surka ga ruwan turaren muski nan zan ba ki. Idan kin yi wankanki na sabulu, to wannan ruwan kuma shi za ki yi wanka da shi a karshe. Hakan kuma za ki yi na tsawon kwse anaki uku, kafin ki bar nan gidan.” Umm Adiyya kam ware idanu ta yi da baki tana kallon Hajja Ku, tana jin bayanan da ke fita daga bakinta. “Wannan kuma jan lalle ne sai da dare, Yalwa za t…