UMM ADIYYAH CHAPTER 73 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 73 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 73 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  shiririta ce sam ba na so. Don haka duk ku tattara ku ba ni wuri, ba na son na saurari kowa. Idan ita Ummu an warware baikon can a kanta, to ni da na bada auren Ummu, ba ni da labari, kai Zubairu kai ne mahaifinta, ban sani ba ko kai ka samu labarin hakan?” A take Abba ya girgiza kansa, yanzu kam ba tantama Zaid ya san iyayen sun hade masu baki ne. “Baffa ku yi hakuri, za mu san yadda za ayi ku ji komai daga bakinsu, amma sam ba zancen wasa da hankalinku muke yi ba.” Ba wanda ya tanka shi, don haka ya dauka a matsayin sun sallame shi ne, kansa ya gama kullewa, a take ya danna wayar Salisu yana fita. “Dan group ka ji abin da muka sa kanmu a ciki, ashe wancan dan Bauchin bai fada masu ya janye ba, yanzu su a dole sun bada Umm Adiyya, ba za su ma karbi batuna ba.”Www.bankinhausanovels.com.ng  “Tijjani sunansa, lokaci ya yi kuma da za ku yi magana ta fahimta da shi, domin dole sai ya sa baki, kafin ka samu Umm Adiyya.” A take wani g…