UMM ADIYYAH CHAPTER 70 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 70 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 70 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  *********** Zaid ya san yakin da yake gabansa a wannan lokacin ba na wasa bane, don haka, bai dauki damuwar Adda Sadiya a matsayin wata damuwar da za ta daga masa hankali ba. Ai ko ya tarar da yaki a ka. “Oho, to, to, to. Wace Ummun kenan?” Baffa ya tambaya lokacin da ya sanar da shi, sun daidaita da Ummu, yana so kuma a ja masa gaba ayi magana. Tunda duka yaran gidan idan an tashi aure, wurinsa ake zuwa tambaya ko kuma shi ya je ya yi. Tun daga lokacin ya san tasa ta same shi. “Baffa, Umm Adiyya dai ta gidan nan, gidanmu. Mun zauna mun yi magana, na fadawa su Baffan Legas da Baffa Mai Kano, to amma kai ma na ga ya dace na zo na fada maka saboda ayi min jagora.” Sarai Baffan yake sane da cewa dan nasa ya bi kan ‘yan-uwansa, shiru ya yi yana so ya ga iya gudun ruwansa. Kallonsa yake yi kamar ya kwada masa mari lafiyayyu. Amma ya daure bai yi hakan ba, “Mun maka kama da shashashu ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng Wani gumi ne ya karyowa Zai…