UMM ADIYYAH CHAPTER 69 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 69 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 69 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Tsuke fuskarsa ya yi, “Ke sai an fara zance na arziki da ke, sai ki koma kuma ki na abin nan.” Dariya ta yi ma’ishinta. Zaid na jin sautin mur- yarta kamar busar sarewa. “I missed you, Twinkle.” “Na sani, ka fada sau casa’in da tara.” “Zan fada sau dubu ma, idan kin ce, ke dai kar ki kara nesanta daga gareni.” “Inshaa Allah, na daina. Kai ma Allah ya kara maka hakuri da ni.” Shiru ya yi yana kallonta, bayan ya koma cikin kujerar ya zauna da kyau, “Uhh! Zubaida ta ce min ki na zuwa ganin Doctor?” Kai ta gyada masa a hankali, ba tare da ta dubi idanunsa ba. Abinda ya fada ne na gaba ya sa ta dago ta dube shi. “Zan iya miki rakiya?” Ya fada yana magana cikin muryarsa mai taushi da zurfi. Murmushi ta yi ta ce, “Zan yi magana da Doc tor din, idan ta amince next zuwa sai mu je tare.” “Na gode.” Daga jin muryarsa ya ji dadin hakan. Wannan ya nuna masa cewa ko ba komai, yanzu wancan zancen ya wuce karkar a wurinta, ta daina kullatarsa da…