TSINTACCIYA CHAPTER 5 BY NIMCY LUV
TSINTACCIYA CHAPTER 5 BY NIMCY LUV
Www.bankinhausanovels.com.ng
Cinyarsa! Wata Ιoyayyiyar ajjiyar zuciya mai sanyi Abbu ya sauke yana lumshe idanunsa, da sauri Akeela ta Ιaga jiΖaΖΖun eyes lashes Ιinta zuwa sama kafin a hankali ta buΙe idanunta tare da sauke Kallonta a fuskarsa Abbu wacce take dab da tashi.
Wani sassanyan Murmushi ya sakar a hankali kuma cikin sakin fuska yace..
“Babyna Daughter na”
Ζuri tayi masa da idanu, saboda kamarsa da Mutumin Ιazo, she’s a cleaver gal amma muguwar taΙararriyar mai saurin kuka, ko dan yawan ciwonta ya sanyata kuka ohhhu?!
Tana da ilimi sosai musamman na addini bata wasa da sallah sam komai tana da tsari.
Murmushi Abbu ya sakar mata yana shafa sumar kanta dai-dai fuskarta yace.
“You’re wake up Babyn Abbunta how do you feel now? Ya jikin?” Ya faΙa yana manna mata kiss a goshinta a hankali ta zame jikinta daga kan cinyarsa tana Ιan marai-raice fuska kamar zatai kuka da sauri tace “no don’t cry kinji” kai ta Ιaga masa tana lumshe idanunta can kuma ta buΙe murya can Ζasa kamar bata son yin magana tace “uhm who are you?” Shafa cikinsa yay kafin ya gyara zamansa tare kama fararan hannunta wanda suke da mugun taushi kamar auduga yace.
“Ok let me introduce myself to you” shiru yay yana kallon tana jin wani irin masifafan yanayi a kanta kafin ya numfasa yace.
“I’m Abubakar Bello, but some of people knowm me as Bukar, I’m the second born Of my parents, ina da big bro but he’s passed away wajan shekaru masu yawa, babban yaya ne shine your father, Isma’il Bello kenan, we lost our father good 30yrs kenan, ina tare da my mother we called her Didi zaki ganta kamar su Ιaya da Aleema, seriously i love her irin sosai Ιin nan more than anything dake nan duniya, bayan ita ina da yara 4 my first son Ιina yafi komai muhimmacin a rayuwarta his name is Abdul-hakeem Bukar Bello zaki iya cewa Yaya, ko hero ko Hamma like yadda Fulani suke faΙa, sai Adnan we lost him shima amma komai ya faru it was a destiny, sa kuma Aleema sai auta Afaf amma yanzu bani da wata Auta sai ke Babyn Abbunta” ya faΙa yana jan hancinta, Ιan Murmushi tayi wanda yasa numfashin Abbu kusan Ιauke wa, domin wannan Shine karo na farko da tayi Murmushi wanda ya haddasa lomawar dimples Ιinta tare da teeths gave Ιinta wacce take siririya sosai, numfashi ya sauke yace.
“Ina da mata guda biyu ta farko sunanta Ayusher we called her Ummi, sai Khadijertou muna ce mata Mami, Nayi karatu mai yawan gaske, ni mai kuΙi ne the richer old man, ada nayi siyasa sosai amma yanzu na sauka, yanzu ina business ne ina da Manyan companies a nan 9ja da kuma Ζasashen waje, ina da manyan contact, Ζwangila kala-kala Allahamdulillah ina duba na Ζasa na ina taimako samuna bai tashi a banza ba, and duk da hakan komai na gidan nan Akeem ke yinsa baya using Kwabo nawa tashi yay ya nema duk yawan dukiyarsa shi ya nema da kansa babu sa hannu na, yana da faΙin rai koni sai nayi da gaske nake juya sa dan yana mugun suna ne yana da biyayya yana da ilimin addini fiye da tunanin mutum I’m so proud of him Wannan shine kawai”
Kallonsa tayi ba tare da tace komai ba shi dai yaji daΙi yana da kirki amma wannan Ιan nashi bashi da mutunci ko kaΙan, har yanzu ta kasa mance abinda yay mata har yanzu kuma tana jin Ζamshin turarensa a jikinta kamar zai zautar da ita.
Bata san mene yasa ba sai kawai ji tayi kuka ya kwace mata, da Sauri Abbu yace “Subuhanallah what happened ina ke maki ciwo” girgiza masa kai tayi tana kwaΙe fuska tare da tura baki gaba “Okey tell me mene ne?” Cikin shassheΖar kuka tace “Baffa na bai so na, he doesn’t care about me zai haΙani da wani mai fitsarin Ζwance and Ζ΄arni Ιin nan zaiwa Aure uhm” ta faΙa tana Ζara fashewa da kuka ita tana ganin ai kamar abin kunya ne a gareta mutane suji za’ai mata Aure wata muguwar kunya ta keji kamar me.
Bakinsa ya buΙe yace.
“No one’s forcing you to get you marriage Babyn Abbu Autata Ohyyyah come here” ya faΙa yana jawota jikinsa tare da fara rarrashinta wani sabon sonta ya ratsa mata zuciya.
Akeela kam ganinsa take tamkar Baffanta Musamman da taji yace shi Ζanin Baffan tane.
Gyara zama Didi tayi tana kallon mutumin tace “Shikenan lashe baki yana tsotse laΙΙansa dan Allah Wannan ai sai ya jamin abin faΙa ko ba haka ba? Mugun hali kuwa bai bar kuwa ba ranar nan balango nace ya siyo min yaΖi to dan Allah ina imani a nan? Taimako nefa abin ma da dukiyar tasa babu san tayaya akai ya rata ta ba, ai ba kayi magana ba ace Hassada bace ba” ta Ζare maganar tana goge hancinta gaba Ιaya mutanan wajan Murmushi suke domin sun fahimci kawai rikicin tsofa ne murmushi mutumin yay kafin yace “In sha Allah Hajiya babba zamu kirasa” da sauri tace “kuce Ubanwa ya faΙa maku a’a babu ruwan ai assurru ma’al sirri koba gaskiya ba, kawai ai faΙa masa ko dan tsire da kaza mai zafi ce yana kawo min” jinjina kai yay yace “to shkknan yadda kikace haka za’ai” tashi tayi Bala driver yana biye da ita a haka suka nufi mota tana shiga ya jata zuwa gida.
A wajan 6 na yamma motar Akeem tayi parking a parking space, P.a ne ya fito tare da buΙe masa Ζofa, gently ya fito da Ζafarsa yana wani lumshe idanunsa tare da sauke ajjiyar zuciya a hankali yake motsa bakinsa yana tasbihi a ransa, ya gaji sosai domin rabin aikin a hospital yay ga program Ιin da zai fara a M.hausa channel, a hankali ya wani ya motsa fuska yana cije bakinsa wani siririn tsaki yaja ganin kallon da P.a ke masa dariya p.a yay kafin yace “Sorry sir” banza yay masa yana shigewa cikin gidan, juyawa p.a yay zuwa gida.
Lokaci daya shiga Afaf ce a Parlo da Aleema sai Akeela dake kwance saman duguwar sofa tana bacci gashinta duk ya rufe mata fuskarta, ga wani Ζaramin Teyana wide-leg trousers dake jikinta sai Applique logo detail t.shirt jikin nan nata sai glowing yake.
Wani series film suke kalla mai suna My perfect husband a zee world.
Da sauri Afaf tace “Wlcm Hero” harara ya watsa mata cikin sauri ta Ιauki remote tare da kashe kallon.
Ζauke kai yay ya nufi upstairs, yana shigewa Akeela ta sauke ajjiyar zuciya yana dafe Ζirji dariya Aleema tayi tace “Laa! so you’re pretending kenan ai kam zan faΙa masa” kwaΙe fuska tayi tana langwaΙar da kanta gefe alamar “No” ba tare da tace komai ba kuma.
Wanka yay ya sauya kaya zuwa Racing jersey da tracksuit trousers, a hankali yake sakkowa daga steps Ιin benen idanunsa a lumshe yunwa ya keji sosai sai baza Ζamshi yake yana tafiya kamar so, kai tsaye kitchen ya nufa domin samun mayen nasa Coffee da ice cream domin ya duba gaba Ιaya ya shanye ice cream part Ιinsa, yana shiga ya rufe Ζofar kitchen Ιin tare da jingina da jikin Ζofar ya harΙe hannayensa a Ζirjinsa.
Tana tsaye a kitchen Ιin tana haΙa tea sai zabga madara take a mug ga kyawawan Ζafafuwan ta a waje Ζafarta sanye cikin wani slippers ga laft tummy Ιinta a lafe ya Ζara fidda shape Ιinta, a sanyaye take komai kamar bata so tana gamawa ta Ιauki mug Ιin tana juyawa idanunta ya sauka a kansa tsananin tsoro da gigicewar da tayi yasa gaba Ιaya ta saki mug Ιin cikin rashin Sa’a gaba Ιaya tea Ιin yay masa ka! Nan da nan fuskarsa tai ja idanunsa ya ΖanΖance ya wani haΙe fuska ta mau a hankali kuma ya fara takawa zuwa inda take tsaye….
Jikin Akeela na wani irin Ιari tayi baya tare da manne bayanta a jikin canter Ιin kitchen Ιin ta wani matse idanunta, laΙΙanta na wani irin KaΙawa tana taune su gaba Ιaya ta jiΖasu da yawo, rawar da jikinta yake ya Ζaro.
A hankali Akeem yake takuwa zuwa inda take fuskarsa a haΙe tamau babu walwala sai Ζwantaccen sajansa dake ta sheΖi tsaye yay a gabanta yana Ζare mata kallo, Ζara matsawa yay kusa da ita very close to her har tana jin yadda Numfashinsa ke fita ga mayataccen Ζamshin turarensa dake dakar mata hanci.
Kamar zai matseta haka ya tsaya a gabanta kafin a hankali ya Ιaga Ζafarsa tare da sauke ta a saman Ζafarta ya wani irin murzawa.
Innalillahi wani irin azaba ta ratsa mata jiki har tana jin yadda Ζashin yatsunta yay Ζara baki ta buΙe zata kuka yay saurin sanya hannunsa tare fisgota jikinsa ya haΙata da Physique chest Ιinsa ya matse ta sosai cikin wata lallausar Muryar mai amsa kowa da sanya mutum zullumi da tarin fargaba yace.
“Shittt!!! Kul Kimin kuka” wani irin matse idanunta tayi wani kalan tsoran Akeem take kamar mutuwa haka take jin tsoransa komai nasa da banne look what he did to her amma yana cewa kada tayi kuka gashi still Ζara murje yatsun Ζafarta yake.
Hannunsa guda ya Ιura akan waist Ιinta ya Ζara holding jikinta a nasa very tight. Ζaya hannunsa kuma yana kan laΙΙansa daya nuna mata alamar tayi shiru Ιib tai shiru kamar ruwa ya cinyeta amma jikinta yana wani irin vibration, ga wani masifafan Ζamshin turarensa wanda yake sanyata jin bacci zuciyarta na wani irin bugu beating fast fast har Akeem na iya jin yadda Ζirjinta ke Ιagawa, ko da wasa ko baiyi tunanin kallon wajan ba domin babu haka a ransa..
Ζara murje yatsun yay da sauri ta buΙe idanunta tare da buΙe baki tace “Auchhhiiii wayyooo Baffana” ta faΙa tana girgiza kanta tare da motsawa zata gudu daga jikinsa yadda kake tsoransa zaka Ιauka ma’aikatan Ιaukan rai ta gani.
Hannunsa dake saman lip’s Ιinsa ya zame tare da sanya hannun ya tallafo haΙarta zuwa wajan fuskarsa fuskar nata yay so cute a hannunsa musamman eyes lashes Ιinta masu mugun tsayi da yawa.
Cikin wata husky kamar wanda akai forcing nasa dole yay maganar yace “kee!!” Da sauri ta buΙe idanunta tare da sauke Kallonta a gashin Ζirjinsa dake kwance fuska ya Ζara haΙewa kamar zai fashe yace “look at into my eyes witch” girgiza kanta tayi tana ΖoΖarin sakar masa kuka cikin wata Ζaramar tsawa yace “heeey!!” Muryarta na rawa tana ΖanΖanme jikinta waje guda tace “Am sorry but I can’t do this” lumshe idanunsa yay sosai yana jin wani abu mai kama da mugunta na taso masa a hankali kuma ya buΙe idanunsa tare da sakar mata wata gigitacciyyar tsawa haΙi da faΙin “keee” Innalillahi tsawar da tayi mata yawa ne da kuma rashin sabo da tayi da ita haΙi da gigicewar da tayi yasa kawai ta faΙa jikinsa ta wani ΖanΖamesa tana sakin maraitaccen kuka haΙi da faΙin “am sorry ha….ban sakewa Hamma Akeemmm!!” Ta jaa! Sunan nashi ta rufe fuskarta a tsakiyar Ζirjinsa gaba Ιaya jikinta rawa yake sosai.
Gaba Ιaya ta firgita da tsawar da yay mata domin tunda take a rayuwa babu wanda ya taΙa yi mata something like this to wama ta sani gaba Ιaya even friends Wannan bata dasu ita Ιaya take rayuwarta ita kam da zama a wajan mutum irin Akeem gwamma ta koma inda ta fito.
Sauke numfashi yay tare da jan wata iska zuwa cikin hancinsa, yadda Jikinta ke rawa yasa gaba Ιaya take neman yarda su a Ζasa, taΖi yarda ta buΙe idanunta balle ga kallesa sai tura fuskarta take cikin Ζirjinsa.
Wani irin taΙe baki yay kafin yay baya kaΙan tare da jingina da canter cikin wata kasalalliyyar murya can Ζasa yace “Uhm hold me tight kafin na Ιallaki” jin haka yasa ta Ζara tura hannunta in between his hammata tana ΖanΖamesa sosai kamar zata koma cikinsa, ganin yadda ta rungomesa irin rungumar nan ta neman tsira da rai rungumar da babu wanda ya taΙa yi masa ita sai Amani yasa ya wani shafa sumar kansa kamar bazai magana ba sai kuma yace.
“Duk abinda nace kice You are” da sauri ta Ιaga masa tana ΖoΖarin zame Jikinta daga nasa yace “don’t ever try” dole ta koma tare da kwantar da kanta a Ζirjinsa tana sauke numfashi a wahalarce.
Gyara tsaiwarsa yay Muryar nan nashi kamar ana buda algaita yace “witch” bakinta na rawa tace “i am” tsaki yaja yana Ζara murje yatsun Ζafarta yace “pairy, mumu jakaness, emty head” wani runtse idanunta tayi sharrrr kuma hawaye suka zubo mata muryarta na rawa tana son fashewa da kuka tace “i am” shafa lafiyayyiyan gemunsa yay yace “aljanar ruwa, Kidnapper mai cin naman mutane Ζ΄ar yankan kai” kuka na kwance mata tace “i am” wani shu’umin Murmushi Yay Wanda ya jima bai irinsa ba kafin yace “Uhmm mai warin hammata” wani raunataccen kuka ta fashe da shi tama kasa magana hannunsa yasa ya zareta daga jikinsa harya juya sai kuma ya dawo ya Ιauki mug ya fara haΙa coffee ko inda take bai Ζara kalla ba, yanzu haka sai yay wanka domin shi da gaske warin take masa sbd rashin tsoran Allah irin na Abdul-hakeem Bukar Bello.
Ya gama haΙa coffee ya nufi wajan Ζofa tafiyarsa ma kaΙai abar kallo ce har zai fita sai kuma ya tsaya cikin wata kakkauran murya yace “ki faΙawa wani kiga sai na bawa karnuka sun cinye namanki” yana faΙin hakan ya fita.
Zubewa tayi a wajan tana sakin wani sabon kukan gaba Ιaya taji ta fara tsanar zaman gidan saboda shi.
Yana fitowa idanunsa ya sauka akan Didi tana zaune saman kujera an Ιura Ζafa Ιaya kan Ιaya tana ganin ta washe baki “kaga irin albarka, kai dai kaji daΙin ka tausayinta kaΙai yasa a soka baka da Ζyashi ko kaΙan shiyasa nace babu wanda zan faΙawa zaka siyo min nama, ato kaf Duniyar nan wa kake dashi mai sonka da sanya maka albarka ai sani Ιin dana zame maka dole na haifi gantalallan Ubanka” banza yay mata yana zaman kan sofa a hankali yake sipping coffee Ιin a bakinsa, Ummi ta fito daga part Ιin Abbu yana biye dashi da alama alwala yay idanunsa ya juya ganin babu Mami yasa ya nufi part Ιin ta.
A can cikin bedroom ya sameta zaune ta zabga tagumi idanunta yay jajir a gefenta ya zauna yana Kallonta a hankali itama ta kallesa kafin kuma kuka ya kwance mata bakinsa ya buΙe yace “come here” da sauri ta Ζara jikinsa tana fashewa da kuka sosai, bai hanata ba sai da tayi mai isarta kafin yace “Mami nasan dole kiji zafi domin ke Ιin uwa ce, duk yadda zanji ciwon abin ba kamar ke ba, amma wallahi bana baccin kirki kullum da damuwa nake kwana, ya Adnan yake? Wanne hali yake ciki? Yana raye? Baya raye? No one’s know, amma dukkan abinda ya samu bawa rubutacce ne daga Rabbil izzati mai kowa da komai, ko da ba’a ce ruwa ya faΙa ba Tabbas zamu nemesa mu rasa, amma har yanzu jikina yana bani Adnan yana raye koma zai dawo garemu in sha Allah, so kiyi hqr kiyi accepting Wannan destiny Ιin you’re muslim a musulmi should trust Ζaddara good or bad ok!”
Kallonsa tayi kamar yadda yake kallonta kafin tace “Abbu ina jin babu daΙi Ζwarai rashin Ιa ba Ζaramin abu bane, kullum ina addu’ar Ubangiji ya kare min Adnan aduk inda yake,amma idan na kalli wannan Yarinyar zuciyata zafi take inside of kai punishing Ιinta akan dalilinta muka rasa Adnan amma ka Ιauke ta ka sanyata cikin yaranka me kake expecting idan wani abu ya samu Ιayan su?” Tunda ta fara magana yake kallonta kafin yace “jinina kike son na wulaΖanta Khadijertou? Ζiyar yayana Baffa zan ci zarafi, ko bayan raina nasan Baffa zai kula da komai na iyali na mene yasa kike son ni naci zarafin tasa Ζ΄ar Ζwaya Ιaya tilo? Please bana so ki barni da masifar da take shirin kunno mini please” shiru tayi masa tana sauke ajjiyar zuciya, MiΖewa yay da ita kafin yasa hannu ya share mata hawayen cikin damuwa yace “Ni Ubane kuma mijine mai adalci, amma hakan ba zai sanya naΖi bin abinda zuciyata keso ke muradi ba” da rashin fahimta Mami tace “Me kake muradi Abbu” hancinta yaja yace “time zaizo Ohyyyah go and pray” “bana yi” zare ido yay yana faΙin “eyee baΖin ciki ido biyu Allah ya Bukar Bello ba’a Ιakin Mami yake ba dana shige” ya faΙa yana ficewa.
A hankali Akeem ya miΖe kai tsaye suka nufi Masjid suna fita Akeela ta fito da sauri idanunta duk yay jaa sosai ga lip’s Ιin nan yay wani pink yirrrrr dashi.
Didi ce ta tafka satali tace “Innahu sulaimanu wa Innahu Bismillahi Meye haka kamar wata munafuka kuma jama’a na shiga uku ke zonan” kwasa Akeela tayi da gudu tana nufar part Ιinsu dan Didi ta iya bala’i da surutan tsofa.
ABUJA
*Aso Rock Presidential Villa*
A hankali ya murΙa handle Ιin Ζofar ya shiga cikin wani makeken bedroom kusan dai gidan Shugaban Ζasa wasting time ne tsayawa description nasa just imagine.
Tsayawa yay yana Ζare mata kallo kafin a hankali yace “Meema” shiru tayi kanta a Ζasa ta tura hannunta a tsakanin cinyoyinta sai sauke Ajjiyar zuciya take..
Wata macace zatai sa’ar Akeem shekarunta kusan 32 amma idan ka ganta zaka Ιauka bata shige 25 ko 26 ba tana da kyau sosai fara tass da ita gashinta ya sauka sosai..
Ganin yadda tai masa shiru yasa ya girgiza kai tare da faΙin “ohh Rabbi ka kawo min Ιauki” ya faΙa a hankali ya gyara zaman babbar rigar jikinsa babban mutum ne shekara wajan 65 to 67 fari ne kamar Balarabe wajanta ya Ζarasa yana zuwa ta Ιaga kanta a tsoro ce domin kullum cikin firgita take kwaΙe fuska tayi har zatai shiru sai kuma tace “Dad” gashinta ya tattare tsaf kafin ya sanya ribbon ya haΙe mata su yace “oyaa stand up” tashi tayi a hankali har yanzu idanunta a Ζasa yace “Your Mom told me har yanzu baki breakfast ba what exactly wrong with my darling eh?” KwaΙe fuska tayi kafin tace “Dad how is he?” Dafe kai yay yace “Ya rabbi Wannan mutumin ba kuwa asiri yay maki ba Meema? Mun tsinci Mutum a hospital daga zuwa zaga marasa lafiya kince dole dole a Ιauke shi na Ιauke sa gashi can ana kula dashi amma dole sai an fita dashi waje” kamar zatai kuka tace “Dad why?” Shafa kanta yay yace “come with me” Kallon Mahaifin nata tayi PRESIDENT AHMED ADIL kenan.
Kama hannunta yay kai tsaye ratsawa yay ta haΙaΙΙan parlon yarinyar tasa kafin ya nufi wani corridor a nan zaka samu main Parlo iya kar haΙuwa ya haΙu wata mata ce zaune tana kallon Aljazeera zatai shekara 54 tana sanye da wata haΙaΙΙiyar shadda ko’ina na jikinta sheΖi yake ga wasu gold a hannunta murmushi tayi tace.
“Ok dake kaine ta kulaka ko yayi” Murmushi Dad yay mata kafin yace “Meema kullum jin kanta take wata Ζ΄ar baby look da aure tayi da wajan yara biyu uku har huΙu gareta” dariya Mom tayi tace “aifa” hannunta yaja yace “bari na karata wajan mutumin Ιan yanzu bazan Ζara barinta fita ba”
“Adawo Lfy Ur Excellency” fita yay kafin ya shiga Elevator kai tsaye kuma da shiga ya dannawa lift Ιin 1floor, tana kusa dashi sai Ajjiyar zuciya take saukewa a haka suka sauka jama’a kuzo kuga haukan securities sai ku Ιauka yaΖin duniya ake, da sauri aka buΙe masu Ζofar wata lafiyayyiyar mota, kai tsaye wani Aso Rock Clinic Gulps suka nufa motar guards na biye dasu.
Sun Ιan jima suna tafiya a cikin gidan kafin su Ζarasa gaba Ιaya guards Ιin sukai masu rumfa Meema dai sai Ιoyewa take domin tsoran mutane take sosai.
A haka suka isa wani Dr ya tarΙesu bayan President Ahmad Adil ya zauna ya dubi Dr yace “Yaya jikin nasa?” Ajjiyar zuciya Dr yay kafin yace “To da sauΖi amma he’s in critical condition sosai” gaban Meema ne ya faΙi da sauri ta riΖe Dad kafin Dr ya Ιura da faΙin “He lost his memory and fuskarsa ma ta lalace baki Ιaya…..
_Ki guji haΖΖin wani domin bala’i ne wallahi sosai fa, idan kina son this book ki siya akan 500 ko nrml grp 300 nidai bazan yafewa dukkan wanda zai karanta bai biya ba haka kukai min akan ABU MALEEK_
Post a Comment for "TSINTACCIYA CHAPTER 5 BY NIMCY LUV"