TSINTACCIYA CHAPTER 1 BY NIMCY LUV
TSINTACCIYA CHAPTER 1 BY NIMCY LUV Www.bankinhausanovels.com.ng Safiyar garin Lahadin yau ta kasance safiya mai ɗumbin tarihi ga dukkan jama’ar da suke yankin Kano kuma a sassa daban daban, Dalilin Kwantaccen baƙin hadarin dake garin, kasantuwar yanayin damu na da muke ciki, kuma farkon watan Agusta. A hankali sassanyar iskar hadarin take Kaɗawa yayinda kuma dukkan baƙin hadarin yaywa samaniya tsinke, cikin nutsuwa baƙin hadarin ke joyewa zuwa jaa, alamar ko wanne lokaci ruwa na iya sauka. Wata ƙaƙƙarfar iska ce mai tafiya da rufin gidaje ta fara fatali da dukkan wasu abubuwa marasa nauyi, ƙarfin isakar da rugugin hadarin ya wuce tunanin dukkan mai tunani da dukkan alama yau ruwan na musamman ne. A hankali kuma gajimaren ke gudu yana haɗa jikinsa waje guda, cikin lokaci kaɗan samaniya tai wani irin jaa wanda ya wuce tunani mutane, ga wata ƙara da rugugi da hadarin yake, wanda ya haddasa tashin tsuntsayen daga saman bishiyoyi zuwa ma ɓoya. Ƙarfin gudun isakar da kuma yadda take fatali da du…