RIJIYA GABA DUBU COMPLETE BY ABDULAZEEZ SANI MADAKIN GINI
RIJIYA GABA DUBU COMPLETE BY ABDULAZEEZ SANI MADAKIN GINI RIJIYA GABA DUBU COMPLETE BY ABDULAZEEZ SANI MADAKIN GINI Www.bankinhausanovels.com.ng BOOK 1 Saurayin gudu yake iya karfinsa acikin dajin domin ya ceci rayuwarsa, . yana gudu yana waigen bayansa cikin tsananin tsoro,amma baya ganin komai kuma baya jin sautin komai face na masifaffun karnukan dake biye dashi. . Su dai wadan nan karnuka sun kai guda saba in da doriya kuma sun kasance jibga jibga tamkar ba karnuka bane kai kace kurayene sabo da girmansu da kwarjininsu gami da ban tsoro,musamman aka kiwata wadan nan karnukan kuma aka basu horo na musamman domin suyi gadin babban kurkuku na birnin Kisra. . A tarihin birnin na kisra tunda aka gina kurkukun tsawon shekaru arba in ba ataba samun fursuna da ya taba guduwa daga cikin sa ba sabo da karfin tsaron da ke cikinsa sai wannan saurayi wanda ake kira IMHAL IBN IMZANU, . sabo da tsananin karfin gudun Imhal ne ya baiwa karnukan tazara ta kimanin taku sittin amma sabo da nacin karnukan da mugun horon da suka samu sai gashi sun fara hango shi,nan fa suka kara kaimi,n…