MALIKA MALIK CHAPTER 4 BY JANAFTY MALIKA MALIK CHAPTER 4 BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng “”Washegari da misalin karfe 10 da wani Abu na Safe Saleem yadau hanyar katsina bayan ya kira Abbi yasanar dashi,shikuma yakira Alhaji Abdulmalik ya sanar dashi ga saleem nan zuwa. Shi ya tuka kansa,shiyasa ya isa akan lokaci domin dama Saleem akwai gudu amota kamar zai tashi sama,koda ya shiga cikin garin katsina bai sha wahalan gane gidan ba,sakamakon gidan Alhaji Abdulmalik Dankasuwa ba boyayye bane a katsina,cikin lokaci sai ga motarsa ta tsaya abakin makeken gidan,wanda yake kama da wata al’karya guda. Hon ya zuba Kafin megadi ya leko yana Tambayansa sunansa kai tsaye yace”Saleem kabir kumo…”Bai yi watawata ba ya wangalemai kofar get din motarsa kirar 4matic ta sulala ciki domin dama Tuni an san da zuwanshi. Aparking space ya Faka motarsa kafin ya Fito yana bin haraban gidan da kallo,wanda wasu tafka tafka motoci iya kallon ka mallam,sukama gidan kwanya gefe daya kuma excorts din Malika keta zagaye suna wani Mazurai Dan …