MALIKA MALIK CHAPTER 1 BY JANAFTY MALIKA MALIK CHAPTER 1 BY JANAFTY Www.bankinhausanovels.com.ng KATSINA_ “””Da misalin karfe 11:20pm na daren Ranar jumma”a Akan Titin dake tsakanin Dutsenmah da katsina wacce take gabda shiga katsina. Adaidai kan Titin akwai yan Sanda wadanda suke patrole awajen,Suna tsatsaye ne Gefe kuma ga motocinsu guda biyu akallah yan sanda zasu kai su Biyar kowannesu, sanye da uniform dinsu bakake,da ganin kayan jikinsu basai ka tambayesu ba,zaka gane dukansu inspector ne,domin basu da kowani Rank ajikin kakin nasu,dukkansu fuskarsu sanye da Hula p-cap,da bakaken safan hannu sai manya manyan Tociloli masu bala”in haske kamar ta yan fashi,wanda in aka dallareka dasu, sai ka dakata saboda bala”in haskenta,Duk motar da tazo wucewa sai sun tsaidata sunyi bincikenta saboda tsaro dakuma bincike, wanda daga sama suka sameshi saboda masu shiga da fita da mugayen makamai wanda ake Shigo dasu daga bodar katsinar aboye. Motocine jere guda goma sha biyu dukkansu 11 din iri daya ne Corollahx sai babban…