MAI TAFIYA CHAPTER 7 KARSHE MAI TAFIYA CHAPTER 7 KARSHE Www.bankinhausanovels.com.ng Karshen alewa kasa!+ With a heavy heart i conclude the last 2 chapters of Maitafiya. Ya Allah ka karbi ranmu muna mai tuba a gareka. Ya Allah ka sa mu gane girmanka da daukakar ka tun kafin lokaci ya kure mana. Allah ka sa mu gyara kurakurenmu tun kafin mu fuskance ka dan darajarka dan darajar fiyayyen halitta. Allah ka raba mu da dattin zina, ka sa mu nisance ta ka sa mu bayyana a gabanka muna tsarkakakku, masu tuba, masu nadama! Ya arrahmar rahimin ya Alkhramal Akhrameen ya zhul jalalu wal ikram.19 Kano, Nigeria Tsaye yake yana kallon agogon hannunsa sanye da farin yadi da takalmi sau ciki. Haka yake yawancin shigarsa yanzu, tsadaddun abubuwa ba su cika damunsa ba. A makarantar yara ta Lufaloy yake, karfe biyu daidai na rana yana hange hangen ta inda yaron zai fito. Yaran ga su nan birjik cikin yinifom, sai ya ga kawai su na yi masa kamanni shigen daya. Bai daina hange hangen ba kawai sai ya ji an ruqunqume shi. ” …