BABBAR YARINYA CHAPTER 8 Oum Aphnan

BABBAR YARINYA CHAPTER 8 Oum Aphnan
BABBAR YARINYA CHAPTER 8 Oum Aphnan Www.bankinhausanovels.com.ng  Cikin sanɗa ya shiga cikin duhuwar bayan ɗakunan ɗaliban ,saida yazo gefenta sannan ya fiddo cillinsa bai tsaya sanya ba ya shiga sakin fitsari a jikin bangon ,Rumtse ido tayi a hankali tanajin fitsarin na taɓa mata rai,wannan wani irin ɗan iska ne wai? Da talallen ƙafa ya nufo gabanta yina faman cinciɗa wando sama da tazuge a hannu ɗaya ,wandon yayi wani rakwakwa gwanin ban takaici ,gabanta yazo ya tsaya. Rimtse ido tayi “Nagode to ban saƙon dare nayi” Murmishi yayi mai sauti ,zuwa ynz daɗewa a duhu yasa sun fara tantance junansu  “Haba dai kura da shan bugu gardi da kwasan kuɗi…? Ai zamuyi ban gishiri ne in baki manda” Zaro ido tayi  “Ban fahimce ka ba wallahi me kakeso kuma?daga taimako?” “Ba wani abu me wuya bane ,taimako ɗaya nima nike nema ki mun ,wallahi shi ya koro ni har na kasa barci in baki taimakeni ba ƙarshe kafin safe kiji anyi janaizata ” kawai sai bakinsa ya fara rawa zai kuka  “A’ah A’ah ,haba kaiko ai kai yayana…