ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Ciki da wannan rana da Allah ya nun min wacce ban bar duniya ba sai da Allah ya nuna min har na zo da kafata na baiwa dan uwana hakuri kan tarin laifukan da na yi nasa, wanda kuma na samu goyon bayan yan uwana, don haka ne ma nake kara neman afuwa a wajensa, Ina neman kuma ku kara tayani ba shi hakuri kan abin da na yi masa a baya Alh Aminu ne ya cafe da “Muka dai yi masa Yaya Ja’a far, ba don na goyi bayan haka ba, ai da abin bana tunanin zai kai mu ga haka. Laifi dai dukkanmu mun yi masa, muna kuma neman afuwarsa. Insha Allah za mu hada kanmu ba za mu sake barin irin wannan ta sake faruwa cikin ZURI’A DAYA ba, da yardar Ubangiji za mu kiyaye sake faruwar hakan Sai Abba ya muskuta kadan ya yi gyaran murya sannan ya ce. “Alhamdulillah, kwarai nayi matukar farin ciki da wannan rana domin ban taba tunanin zuwanta ba ma ko a mafarki, saboda a yadda nake hange da tunani, ban taba kawowa a raina wannan ranar ma za ta zo ba, gan…