ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya ka fice min daga gida. Yaudarar da ka yi min ta nuna cewa koya maka aka yi, don haka ban yarda ka Kara min ko minti guda ba cikin minti biyar din nan. Kada na fito naga Keyarka a nan. Mustpha wuce mu je” Www.bankinhausanovels.com.ng Tsananin mamaki ne ya bayyana a fuskar Sameer, ko kadan bai taba tunanin haka ba daga wajen kawun nasa. Tunda ya ke bai taba ganin tsana a fuskar wani mutum ba irin wacce ya gani yau da aka nuna masa. Sai dai ko kadan ransa bai baci ba, domin duk abin’ da ya yi masa bai ga laifinsa ba, don hakan ya nuna har yanzu ya na cikin fishin. Kuma duk wanda Zur’arsa za su yi masa haka dole ne ya yi fiye ma da hakan. A ta ke shima ya ji ba zai iya zama a cikin Estate din ba. Kai tsaye kawai ya juya zuwa Kaduna domin ya fadawa iyayensa su san abin da za su yi su kori wannan bakar gabar domin ya na ganin abin ya fi Karfinsa. ****** Kwancce ta ke akan gadonta ta yi ruf da ciki sai k…