ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Haana da Rauda sun zama abin tararaiya a‘cikin Zuri’arsu, kowa da irin so da Kaunar da yake ba su. Haka sukejin farin ciki na Kara kamasu, sam ba ma za ka gansu tare ba saboda daga wannan ya ja wancan, sai wannan ya janye wancan sai kuwa suka dinga jin dadi. Abin da idanun Haana ya ke mata shi ne gizo, duk wani da namiji da yake cikin zuri’arsu sai ta ga ya na yi mata kama da Malam M.J, musamman Alh Ja’afar, don ranar ma da ta ganshi sai taga kamar ‘ M.J dinta ta gani. Da kanta ta yiwa kanta fada cikin zuciyarta na cewa. Mene ne za ta damu da shi bayan ma ya tafi ya barta cikin kewarsa, amma ya barta sai ganin kowa ta ke yi kamar shi. Da sauri ta cire wannan magination din da ya ke yawo cikin ranta ta fara fadin. “Allah sarki Malam M.J na, yau ga shi na cika burina na ganin hadin kan Zuria’ata, na kuma hadu da su. Zamannan kuma da na yi da su sai nake jin kamar na Karasa sauran rayuwata da su. Na…