ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 14 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 14 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Suna cikin haka sai ga Granny nan da Ya Abba suka shigo dakin a rude suna tambayar me ke damunta. Ganin yadda kowa ya rude a kan jin rashin lafiyarta duk sai ta ji tausayin su ya kama ta a ranta ta ce da za ku ji dalilin ciwon nawa da dama daga cikinku babu wanda ba zai ji haushi na ba, malam M.J me yasa ka yi min haka? Me yasa ka kasa gane cewar nima tuni na kamu da son ka kamar yadda ka kamu da son ‘yar uwarka ba ka yi wa ZUCIYA DA RUHI na adalci. (Sunan littafin Sa’adatu Waziri mai fitowa nan gaba idan Mai duka ya yarda). Tana jin likitan da ya zo duba ta yana fadawa Abba cewa damuwa ce ta yi mata yawa ga kuma wata damuwa da take son jefa kanta a ciki. Haba jin haka Abba ya shiga jero mata tambayoyin cewa me yake damunta da za ta boye ta ki gaya musu? Ba ta samu damar ba shi amsa ba likitan ya ce, damuwar zai iya yiwuwa a kan karatu ne. Sai lokacin Abba ya dan ji sanyi don ya san halin diyarsa da naci a kan karatu mutuk…