ZUMA CHAPTER 6 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 6 BY SHATUUU
ZUMA CHAPTER 6 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  A lokacin bayan yayi hanging da zaa bude muku zuciyata ji nake kamar gobara takeyi, tamkar wuta ake rura min haka nake jin wani zafi, gaba daya se jikina shima ya dauki zafin, nan na kwanta akan gado inata kuka ko zan samu naji zuciyata tayi sanyi.+ A bangaren Aliyu yana office na sanar mishi da halin da ake ciki, kawai se ya mike ya fita daga office ya cewa messenger dinshi duk wanda yazo yace dashi ya fita. Seda yayi exiting gate din baki daya sannan ya tare me napep yace ya kawo shi Aminu kano, a ganin shi sanin halin da nake ciki shi ne number one priority dinsa amma Fatima kam ita nata case din me sauki ne. Yana zuwa ya kirani a waya amma seda ya kira for more than seven times ban dauka ba, sunan shi ma bacin rai yake saka min. Ina ganin a gurin shi shine karon farko da yaga rigima ta, ni kaina nasan hankalin shi a tashe yake amma a lokacin ko a jikina,kullum ranar duniya faranta masa nake, kullum rana am making sacrifices for …