ZABI NA CHAPTER 16 KARSHE BY FADEELARH ZABI NA CHAPTER 16 KARSHE BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng FLASHBACK!!! A lokacin da su Ameera suka ji labarin hatsarin Layla an sanar da su cewar tana raye amma unconscious don haka su je asibitin St Gerrard. Ba tare da bata lokaci ba Zayd da Ameera suka nufi asibitin.. A asibitin ne ake sanar da su cewar wadanda suke tare a motar duk sun mutu.. Wato Haleema da Tukur! Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. Haleema ta rasu ba tare da ta gyara hali ba, ta rasu tana kan hanyarta na aikata mummunan aiki.. Ya Allah kar ka sa mu zamo masu aikata munanan ayyuka a duniyan nan Ameen.6 A yadda labari ya zo daga eye witness an ce tyre ce ta fashe shine motar tayi losing control ta fada daji.. Ko da suka samu ganin Layla ta farfado kuma bata wani ji ciwo ba domin kuwa kanta ne da ya dan bugu sai targade da tayi a hannu da kuma scratches here and there on her body… and she had already been treated accordingly. Babu abinda take rusawa banda kuka jin cewar qawarta Haleema ta ra…