ZABI NA CHAPTER 14 BY FADEELARH ZABI NA CHAPTER 14 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng DAYS LATER+ Tuni su Abba sun koma sabon gidan su a cikin Malali GRA. Abba dai har sai da Abbu ya sa baki a maganar sannan ya amince. Ginin bene ne sashe uku sai boys quarters da kuma quarters na masu aiki. Abba ya dauki sashe daya, Umma ma sashe daya sai Mama da Layla suma sashe daya. Su Ibrahim kuwa suna boys quarters abin su. Da qyar Abba ya amince ya karbi motoci biyu a cikin guda uku da Zayd ya bashi… Shi dai Zayd bai takura shi akan wannan din ba. shi kam burin shi ya cika tunda dai ya sanya sirikin nashi cikin irin rayuwar da yake so. Gidan Abba dai ya masifar haduwa.. Gida kamar Zane saboda kyau.. Duk wani abin zamani na jin dadi akwai shi a wannan gida. mai karatu ba sai na baka labarin kyan tsari na wannan gida ba.. na barka ka cigaba da fantasizing. Abin mamaki kuwa Mama sai washe baki take yi tana murna ta shiga daula.. haka ta dinga gayyatar qawayenta ‘yan qarya suna ta zuwa suna ganin gida.. Hatta Hajiya Suwaiba ta zo…