ZABI NA CHAPTER 12 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 12 BY FADEELARH
ZABI NA CHAPTER 12 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA+ Wuraren qarfe tara na dare Ameera tana tsaye a gaban daya daga cikin wadrobes din dressing room na dakinta daure da towel… Da alama wanka tayi. Basu dade da dawowa daga gidan Abba ba.. Ko da Zayd ya koma gidan Abba zama yayi akayi hira sossai harda Abban.. Sai da suka yi dinner sannan suka bar gidan.. Ita kuwa Mama tana can cikin daki tana ta faman lallashin ‘yarta wadda duk ta bi ta haukace.. Ta qarfafa mata qwarin gwiwa akan lallai da zarar Hajiya Suwaiba ta ga Malam toh lallai Hanya zata yi musu kyau. Ko da suka shigo gida kuwa Ameera wucewa tayi straight sashen ta don yin wanka. Ameera tayi kusan minti biyar tsaye tana qare ma kayan baccin ta kallo.. Kayan bacci ne kala-kala har basu qirguwa.. Zaheera, Zarah da su Maheera ne suka jera mata su a wadrobe din tare da sauran kayan lefenta.. idan ka bude wadrobes din ka ga yadda aka jera kayan zaka yi zaton na sayarwa ne aka jera a shago…