ZABI NA CHAPTER 11 BY FADEELARH ZABI NA CHAPTER 11 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng 3 days Later.. AHMAD MUHAMMAD FADOUL RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA+ Kwance take a cikin Duvet a kan gadon dakin tana ta kuka yayinda Zaheera take zaune a gefenta tana lallashinta. Tun ranar da ta farka aka sanar da ita komai ta birkice musu.. Roqon Abba ta dinga yi akan a warware auren don ita ba Zayd din da take so bane wannan amma sam Abba ya qi sauraron ta. Gaba daya yinin ranar ana ta faman lallashin Ameera amma ta qi sauraron kowa.. Wannan abu ya ba Aunties dinta mamaki sossai.. Zarah da Zaheera tare da ‘yan biyu kuwa har rasa bakin lallashi suka yi.. Ammi ce ma tayi qoqari ta shawo kanta har ta daina kukan da take yi amma fa ta qi yi ma kowa magana musamman Zayd wanda da zarar ya shigo dakin nata sai ta juya mishi baya tayi kamar tana bacci.. haka yake zama yayi ta mata magana yana bata haquri amma sam bata ce mishi komai. Sossai wannan abu ya dame shi.. Da ka gan shi a ‘yan kwanakin zaka gane yana da damuwa. Ko da ya ga abu ya q…