UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 20 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 20 BY SHATU
UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 20 BY SHATU Www.bankinhausanovels.com.ng  Seda Junaidu yayi kwana uku baya zuwa ko kofar dakin Hajja indai ba wanka zaiyi ba ko Kuma dai wani Abu zai kaishi bayi din,  abinci ma har daki take kawo mishi yaci, sede yayi ta juyi Alan gado, kannen shi ma har adduar ya samu sauki suke Masa ko ya fita a dakin su samu sararin zama, Amma da sun shigo kwakwaran motsin da Bai gamshe shi ba zasuyi ya dinga zaginsu, ko ya wurga musu abinda ya fi kusa dashi. A kwana na hudu ya fito daga daki zai je wanka, Hajja sake zaune tace+ ” Junaidu dawo Ina son magana da Kai” Ba tareda ya juyo ba yace ” Wanka zanyi ki jira na fito” Ya saka kanshi ya nufi toilet, Fatima ta Gama hada ruwanta me zafi ta Kai toilet zata yiwa Yara wanka, ta manta Bata matsa musu toothpaste a brush dinsu ba, shikuwa Yana zuwa ya wuce ciki ya turo kofa ya fara wanka, Babu jimawa ta dawo hannunta dauke da bar of soap, ta Dan tsaya ganin toilet din a rufe tace da zainab dake kusaa da gurin ” Waye ya shiga toilet…