UMM ADIYYAH CHAPTER 63 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 63 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 63 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Eh, tabbas laifi ne mai tsauri, zai iya yiwuwa ya gaza danne kwadayinsa, zai iya yiwuwa yana son ya balle ya gina nasa kam- fanin ne. Har hakan ya janyo ya yi abinda ya yi. Yana da iyali, matarsa kuma tana kirana kaninta. So, ya biya tarar da aka ci shi, ya dawo kuma da wasu daga cikin kudaden da ya samu daga hannunsu. Yanzu haka yana kirana duk karshen wata ya fada min abinda yake ciki a sabon wurin aikin sa.” Yallabai gaskiya kun yi kokari, ba kowa ne zai iya abinda ku ka yi ba. Allah ya saka maku da alheri.” Gefen labbansa ne suka motsa sama kadan, alamar murmushi. Suka ci-gaba da hada wayoyin da suka dace su y. A nan dai aka yanke shawarar washegari za su gamu da kamfanin N-Bits. ********** Hankalinsa gaba daya ya tafi akan wayar da yake yi, ya bada dukkan natsuwarsa a kai, lokacin da ya ji ana taba kofar ofishin nasa alamar kwankwasawa, idanunsa ya mayar kan komfutar da take dauke da hotunan mutanen, Karamin falon karban baki…