UMM ADIYYAH CHAPTER 61 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 61 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Ina, sai dai ki gwada mata ja da mulmulewa. You’re just too adorable (ke abar so ce, har ma kin kure).” Www.bankinhausanovels.com.ng Da ya gama ta kalli kanta, a madubi ta tuntsure da dariya saboda guda biyu ya kukkulla mata, suka yi kama da kahon rago. Har yanzun da yake tuna wannan lokacin, sai dai ya ji gudun zuciyarsa ya karu. “Kin faye shiga rai Twinkle.” Ya fada hade da shafe kan wayar, nan ya shiririce da kallon hotunanta, wasu ya yi dariya, ya girgiza kai wasu kuma ya yi tsam zuciyarsa ta cika dam! Da abubuwa masu nukurkusa wannan tsokar. Lokaci guda ya fita daga wurin hotunan gaba daya. Ya runtse idanunsa ya hadiyi wani abu hade da maida kansa jikin filo. “Good night, Twinkle.” *********** Juyi ta yi a kan gadon, ta dago kanta cikin saurare, gabanta ne ta ji yana yawan faduwa. Wannan ya sa ta mike ta mutsuke ida nunta ta shiga bandaki ta dauro alwala. Nafila raka’a biyu ta yi ta dade tana ad- du’o’l, cikin sujjadarta, …