UMM ADIYYAH CHAPTER 60 BY AZIZA IDRIS GOMBE UMM ADIYYAH CHAPTER 60 BY AZIZA IDRIS GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Oh Yaya Salisu, yaya gida da su Aunty Mashkura?” “Alhamdulillah! Suna Kalau, uhm na shigo Bauchi ne jiya da dare, ban sani ba ko ki na gidan yar kin nan ne na (Airport Road)? Akwai maganar da na ke so na zo mu tattauna.” Ummu Adiyya ta yi shiru tana Www.bankinhausanovels.com.ng nazari, to ita kuma? Wace irin magana ce hakan kenan? “Wani abu ne ya faru?” “A’a ba komai, idan dai ki na nan ko za ki ba ni lokaci sai na zo anjima?” Eh ina nan.” “To shi kenan na gode. Allah ya kai mu.” Ameen.” Ta fadla, sannan ta cire wayar a kunnenta cikin nazarin ko menene hakan? Surutun Safiyya ne ya dawo da ita daga guntun nazarin da take yi. Dakin Adda Zubaida ta shiga, ta samu ta idar da karatun Al-Kur’ani. “Adda ga ta, bari na yi wanka, idan na bar ta a aki, aiki za tai min da turare ko jambaki.” “Ki rinKa dorawa a sama ai kawai, idan ba haka ba, haka za ku rinKa fama.” “Cab! Yarinyar da ta iya darewa kujera ta za- una kan ma…