NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 10 KARSHE

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 10 KARSHE
NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 10 KARSHE Www.bankinhausanovels.com.ng  _______bayan wasu shekaru. Zaman aure na nike mai kyau da tsafta da kuma tsantsar so da kulawa da junan mu, alhamdu lillah na kammala secondary school di na , amma ban samu na cigaba ba, saboda yah Sadeeq irin mazajannan ne masu bukatar iyalan su a kusa dasu, kuma yace “mai zanyi da karatu mai zurfi indai zan karanta na rubuta kuma na fadi a fahimta nima idan an fada min na fahimta ai shikenan” .+ Mun samu fahimtar juna sosai tsakani na da yah Sadeeq zan iya cewa tundaga ranar da aka kaini har kawo yanzu da nike magana baiyi abunda zai cusguna min da gangan ba, saida bisa rashin sani da kuskure wanda dama dan Adam tara yake bai cika goma ba, yah Sadeeq mutum ne mai saukin kai da tausayin na kasa dashi yanzu haka mun bude gidauniyar da ake temakawa marayu da gajiyayyu. Ya rike mukamai da dama a bangaran aikin sa yanzu haka shine kwamishinan yan sanda na nan jahar kaduna, mun haifi yara yan biyu duka maza shekarun su uku yan…