ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  ba kowa bane illa abokin fadanta a bakin (gate), mutumin da ya buga mata motar ta ne. Bude baki tayi domin nuna tsananin ~ mamakinta da ganinsa, ashe dama shi ne malamin nasu da ake fada ne? Yau ta shiga uku, ya zata yi da tarin tsaurin idanun da tsiwar da tayi masa dazu?” Shima kallon nata ya yi mai cike da mamaki, to amma sai ya Boye ya nuna kamar bai ganeta ba. Shiru (lecture hall) din ya yi sannan ya yi gyaran murya, ya shiga ya yi dan dube-duben sa cikin I-pad dinsa, sannan ya ce. “Salam alaikum (class)”. Duk aka amsa cikin sakin” fuska, sannan – ya soma da cewa. .”Don Allah ina neman afuwar ku na rashin zuwa na da wuri, wata ‘yar tangarda na samu hakan ya janyo na makara”.Nan take aka amsa da, “Babu matsala Sir”. Amma ban da Haana, domin duk jikinta. ya yi sanyi don bata san da wane ido zata iya dubansa ba, domin zai yi tunanin bata da kirki, ya zata sam bata da tarbiyya kamar yadda wannan…