ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Sai dai wani abu da yafi daga mana hankali yadda Hameed ko da yaushe sai ya zo gidanmu yana roKon son ganin Aziza don ta yafe masa, amma ba ma barin ya ganta, domin itama ta Ki bari su hadu. Tsananin ramar da yayi da nacin da yake nunawa hakan yasa tausayin sa ya fara shigar mu ni da Ammi ku, domin kallo daya zaka yi masa ka gano ba ya cikin kwanciyar hankali. Duk ya rame ya yi baKi, ya zamo baya iya komai, bashi da wani buri da ya wuce ganin Aziza, amma ina! Baya samu, komai na rayuwar sa ya tsaya cak, ya daina yin komai, haka ya zamo abin tausayi tsabar tsananin damuwar da yake ciki. Ba don dokar da Mustapha ya samana ba da tuni mun bar Hameed sun hadu da Aziza, to . amma ya Zamu yi? Dole haka zai zo ya Karaci surutansa ‘da sambatunsa ya hakura ya tashigudun kada Abban ki ya dawo ya same shi. . Tun yana jin tsoron dawowar sa ya same _ shi ya zamana sai ya dawo ya same shi anan, ~ amma. ba zai k…