ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya Jin furucinsa sai abin ya bashi mamaki, domin bai tambayi halin da diyarsa take ciki ba sai wannan maganar ya jefe shi da ita. Nan take yaji ransa ya baci, amma sai ya tuna shi din gaba yake da shi, dole yana girmama shi tun da sun taso da wannan tarbiyyar a gidan su. “Yaya banyi tunanin cewa da wannan maganar zaka fara yi min ba, tun dazu muka dawo babu wanda ya zo ya duba jikin Aziza amma sai gashi ka aika an kirawo ni saboda wani dalili”Daga masa hannu yayi, ya ce, “Dakata Mustapha, dole dama zan yi maka wannan maganar, amma tunda wannan ita ce a gabanmu ai dole na fara yi maka ita ‘saboda ita na kira ka. Shin ka janye ko baka janye ba?” Ransa ya baci, yace, “Yaya dole zaka yi . min ko UMARNI kake bani akan dole nayi abin da kake so?” Girgiza kai yayi, ya ce, “Ko kusa ko alama, idan ban tilasta ka ba to kai ka tilasta kanka ka janye ko kuma kai a kai ka Kara saboda wasu dalilai da kai ka sani …