ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 17 KARSHE BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 17 KARSHE BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 17 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Mun tsaya Haaya ba, hakan yasa ya yanke shawarar nuna mata jan ido don tayi fishi ta haKura da shi. Sam ba wai baya son Haaya bane, tana da kirki da nutsuwa ya yaba da tarbiyyarta. Www.bankinhausanovels.com.ng Sai dai kash! Babu wanda zai samu wani matsayi a cikin zuciyar sa idan ba Haana ba, don ko kadan babu wata mace da zuciyar sa take so da gani idan ba Haana dinsa ba, don haka ya yanke shawarar sulalewa ya bar Kasar ba tare da _~ Haaya ta san shirin sa ba, domin idan ya tsaya tausaya mata haka zai yi ta zama ba tare da ya duba abin da ya dace da rayuwar sa ba. Ya Abba fari ne shi sosai kamar ka taba hannunsa jini ya fito, kana ganinsa ka ga Bafulatanin asali. Suna matuKar diban kama da haana sosai da sosai, domin duk kamar mahaifin Haana suka debo, domin tun yana jariri yake kama da Alh. Mustapha, wannan yasa Kanwarsa Maryam ta yiwa yayanta takwara. . Dogo ne shi sosai amma mai dan jiki, gashi baki ne ke da shi, a fuskar…