ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya daga idanunta sai ta ga sun hada idanu da Malam M.J, lokaci guda kowannen su ya yi saurin dauke idanunsa daga kan juna. . Murmushi tayi cikin ranta ta ce, “Mugu, Allah Ya fika, gashi nan wanda na zo nema yazo, kada kayi tunanin zan zo na tambaye ka wani abu tunda kasan neman wani abu na zo. Kaje kayi ta tsare gidan ka wanda babu inda zai kai ka”. Ta saki tsaki cikin ranta. Tana ganin Malam Yusuf ta saki ranta hade da murmushi, zata mike ya daga mata hannu akan ta zauna bari ya Karaso. Ta ji dadin hakan. . . Guri ya samu ya zauna, nan ta fara gaida shi cikin ladabi da murya Kasa-Kasa, ya amsa cikin fara’a. Sun fara magana kenan sai ta ga ya mike, yace “Ina zuwa, bani minti daya”. Kafin ta bashi amsa har ya mike, gurin Malam M.J ta ga ya nufa, ga mamakinta sai ta ga sun daga hannu sun kashe, take ta ga sun rungume juna cikin farin ciki. Ga mamakinta sai ta ga ya ja hannunsa za su fita, ya zo gurinta…