ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 16 KARSHE BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 16 KARSHE BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 16 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya A rude ya ce, “Umma wai me ke faruwa ne? Shin Ammi na ta warke ne? Wai me yake faruwa ne? Ni fa na rude naji tana kiran Hameed, me Hameed din ya zo ya yi? Ko an ganshi ne?” Abba gani, dama ba bata nayi ba”Gaba dayan su suka juyo suka kalli bakin Kofar shigowa inda suka jiyo muryar sa. Hameed ne tsaye bakin Kofar yana mai Kokarin shigowa. “Kada ka sake ka Karaso nan gurin Ya Hameed, na tsane ka, ba zan taba yafe maka ba, macuci, azzalumi, mara tausayi. Wallahi sai Allah Ya saka min abin da kayi min”. Tana fadin haka ta fashe da kuka tayi sauri ta hangi wani kwalbar lemo ta dauka da sauri ta je ta doka masa a goshin sa, nan take jni ya wanke fusakar sa. Kowa na gurin kasa motsi ya yayi, ana tsaye ana kallon ikon Allah. Nan da nan Mustapha ya Kara rudewa domin har yanzu bai fuskanci inda suka dosa ba. Hameed yana tsaye yana mamakin furucin Aziza nan take ya gane cewa tunaninta ya dawo, Www.ba…