ZABI NA CHAPTER 5 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 5 BY FADEELARH
ZABI NA CHAPTER 5 BY FADEELARH                     Www.bankinhausanovels.com.ng  GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH MALALI+ Layla ce kwance a kan gadon dakin su tana video call da Habib.. A lokacin Ameera tana tsaye gaban wadrobe dinta tana jera kayanta da ta wanke ta goge.. tana jera su yayinda take feshe su da turare daya bayan daya. Ameera dai tana aikinta tana sauraron Layla da yadda take ta hira da Habib a waya.. “wane irin Birthday party ne all night long sweetheart??? Gaskiya fa Abba bazai bari in kwana a waje ba” “Yanzu Pretty birthday party din nawa ne zaki kasa zuwa?? toh meye amfanin yin party din babu ke??? besides na fadi miki Leema zata zo and zan so inyi introducing dinki to my friends.. please dont say no” “Sweetheart wallahi zan so zuwa.. kawai dai babu hanya ne..” “Ke yanzu duk dabarun ku na mata kina nufin you can’t come up with something?? I swear sometimes sai in dinga gani kamar son da kike yi mun ragagge ne…” “Haba sweetheart.. kar kace haka mana. Yakamata ka san cewar ina son ka…