ZABI NA CHAPTER 4 BY FADEELARH ZABI NA CHAPTER 4 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng Days later! HABIB ALIYU NASIDI RESIDENCE MARAFA ESTATE+ Zaune suke a tangamemen falon gidan shi suna ta hira. Yawancin hirar tasu duk ta ‘yan mata ce da kuma rayuwarsu ta sharholiya da suka dulmiya a ciki. “abokina wallahi ta matsa mun akan lallai Abbanta yace inyi introducing kaina kuma gaskiya I am scared.. ya kake gani ne???” Yusuf wanda yake kwance kan doguwar kujera 3-seater ne yace “gaskiya kar ka kuskura ka je don kuwa duk ranar da ka samu Layla kamar yadda kake so sannan daga baya abubuwa suka dan birkice za’a yi tracing dinka. Ni na rasa meyasa ka kasa exploring dinta har yanzu.. yau fa sama da wata daya kenan da haduwar ku. Haba Habib.. ni da na san ka at most 3 days ka aiwatar da komai amma ace ka kasa yin komai har yanzu” Habib ya dan sosa kan shi yace “ai baka gane ba, yarinyar tana da dan taurin kai ne.. dukda she is a bit loose ina gani kamar upbringing din da aka yi mata was kind of strict.. a hankali nake bin ta don…