ZABI NA CHAPTER 3 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 3 BY FADEELARH
ZABI NA CHAPTER 3 BY FADEELARH                     Www.bankinhausanovels.com.ng  KADUNA STATE UNIVERSITY+ A yau ne wani saurayin Haleema mai suna Yusuf Suleiman Mayana zai zo ganin ta. Asali yakamata ya je gidan su ne amma kuma tafiya ta taso mishi zuwa Russia wanda mahaifin shi ne ya aike shi don haka ne zai zo school don suyi sallama. Yusuf dai yana cikin samarin Haleema da take ji da shi domin kuwa gayen yayi ne ta ko’ina. He is handsome, rich and sophisticated. Tana zaune a garden tare da qawayen ta ne ya kira ta a waya tayi mishi kwatancen inda take. “Yau dai Layla zata ga Yusuf dina.. ” cewar Haleema. Layla tace “tabbas yau zan gan shi.. na kula kina ji da shi ai..” Yusrah ta tabe fuska tace “hmm.. ni kam duk gani nake yi bata lokaci ne tsayawa sauraren samari idan ba wai na shirya auren bane” Maryam tana dariya tace “Yussy kenan.. Allah dai ya kai mu ranar da wani zai sace zuciyar ki, I swear we wont hear word” Suna nan zaune suka hango shi a parking lot inda ya faka motar shi. Wata dall…