ZABI NA CHAPTER 2 BY FADEELARH ZABI NA CHAPTER 2 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng Bayan wata daya da auren su ne Sameera tayi shawara da Farouq akan tana so ta fara sana’a da kudin gadon ta.. ta tsayar da shawarar fara kunun aya saboda ta kula mutane suna siya sossai..+ Yayi farin ciki da jin hakan. Ya tabbatar Sameera ba lazy mutum bace kamar Hindatu. Nan da nan ta bayar da kudi aka siyo mata ‘yar madaidaiciyar deep freezer, buhun aya da na sugar, bottles, flavour da duk wasu abubuwan da zata buqata. Tuni ta fara yin kunun ayan ta.. tayi ma makwabta talla… Kunun ayan Sameera yana da masifar dadi.. hakan ya sanya nan da nan kasuwa ta bude mata. Idan tayi kunun aya kafin kace kwabo ya qare. Duk qarshen wata idan ta hada ribarta sai ta ba Farouq ya zuba mata a account dinta. Hindatu dai tana nan zaune babu aikin fari bare na baqi.. sai tijara da baqin hali. Sossai Sameera take son Layla amma Hindatu ko daukar ta bata bari tayi.. Haka Sameera zata shiga kasuwa ta ga abubuwa ta siyo ma Layla ta kawo kuma babu kunya s…