ZABI NA CHAPTER 1 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 1 BY FADEELARH
ZABI NA CHAPTER 1 BY FADEELARH BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM ✍ZABI NA✍ ☆☆☆☆☆☆ Babban abin da yake janyo wa wasu ‘yan matan rashin samun mazajen aure shine ruwan ido. Da yawan ‘yan mata yayinda suka kai wani mataki na girma, tauraruwar su na haskawa a wannan lokacin.. Hakan yana sanyawa samari su dinga tururruwar zuwa wajen yarinya don zama masoyinta na aure da wanda ba na aure ba….+ A wannan mataki ne ita budurwar take ganin ta zama tauraruwa wanda hakan ya kan sa ta ruwan ido wajen zabar masoyi na qwarai kuma na gaskiya wanda yake sonta tsakani da Allah. ‘Yan matan su kan zabi masoyi, Idan kuma suka samu wanda ya fi shi sai su canza… haka zasu yi ta canzawa har su rasa wanda za su zaba. Rudin duniya ya kan saka idanuwansu rufewa su rasa gane ina suka dosa. Ba wani abu bane yake janyo hakan… illar KWADAYI da kuma SON ABIN DUNIYA shi yake kawo hakan Wani lokacin ma da karance-karancen littafin Hausa da yake tasiri cikin zuciyarsu.1 Da yawa a yanzu sukan dauki buri mai girma su dorawa kansu wanda ha…