YAR NAJERIYA CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR YAR NAJERIYA CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng Tana kudundune cikin zanin Inna a can karshen gadon bonon ta, rabin gashin kan ta ya fito, wanda ba baki bane gabadaya, a kwana biyu kacal tayi mugun ramewa, ‘yan idanun sun kara kankancewa daga ‘light-blue’ sun koma ‘ash colour’. Ba zaton ta ba tsammani, kawai sai ganin Uncle Saheeb ta yi a gaban ta. Ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu staring at her straight in to her eyes with so much sympathy and pity, bai zauna ba daga tsaye motsa baki yace “HASNAH!” Saukar muryar sa ke da wuya cikin kunnen ta da gangar jikin ta, sai ta ji duk wani rauni na duniya da maraicin duniya ya rufto mata….. ‘this is indeed a shoulder to lie on’, zata so ta kwanta a wannan kafadar… tayi kukan ta mai isar ta a inda ta san za’a lallashe ta a gaya mata mai dadi, amma babu dama tunda ta san ba muharramin ta ba ne ba. Kawu sai ya kasa tsayawa tare dasu ganin sai kallon juna suke bakin sun a motsi idanu fal hawaye,…